By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 19 ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis a wani hatsarin mota da ya afku a Bagauda, kusa da harabar makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya.
An gano cewa hatsarin ya afku ne a lokacin da wasu motocin bas guda biyu na kasuwanci Toyota Hiace, masu lambar rajista KBT 152 XA da kuma mai lamba NSR 275 ZX suka yi karo.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya Zubairu Mato, wanda ya tabbatar wa manema labarai hatsarin, ya bayyana cewa hatsarin da ya rutsa da fasinjoji 45 ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 26 suka samu raunuka daban-daban.
A cewar Mato, an kwashe wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kura domin kula da lafiyarsu, yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka mutu a ofishin ‘yan sanda na Bebeji dake jihar Kano.
Ya ce, “Mun samu kiran waya da misalin karfe 7:30 na safe. Da samun labarin, mun yi gaggawar aika jami’an mu da motar mu zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto wadanda abin ya shafa.
“Jimillar fasinjoji 45 ne a cikin motocin bas guda biyu wadanda hatsarin ya rutsa dasu, 19 sun mutu (manya maza 14, manyan mata hudu da yaro namiji daya), yayin da wasu 26 suka samu munanan raunuka.
“Hatsarin ya faru ne a sakamakon wuce gona da iri, tukin ganganci da kuma rashin tsaro, lamarin da ya kai ga yin taho-mu-gama, inda motocin biyu suka kama da wuta nan take, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 19, yayin da wasu 36 suka samu raunuka daban-daban. .”