Rahotanni sun bayyana cewa wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne da kuma barayi sun tsere daga dakin a jiye masu laifi na yan sanda da ke Egume a karamar hukumar Dekina na jihar Kogi a jajibirin sabuwar shekara.
Mutanen biyu da ake zargi da aikata manyan laifuka ana zarginsu da hada baki da wasu tare da kwace makamai daga hannun ‘yan sandan da ke ofishin kafin su tsere.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ce, aka dauke wanda ake zargin mai garkuwa da mutane kwanan nan ne daga sashin ‘yan sanda da ke Lokoja zuwa ofishin ’yan sanda na Egume, inda ake tsare da shi bisa laifin yin garkuwa da mutum da kuma kashe shi.
Mutum na biyu da Jaridar Daily Trust ta gano shi ne mai taurin kai, wanda ya kware wajen satar kayayyakin wutar lantarki.
An ce wasu ‘yan banga na yankin sun kama shi makonnin da suka gabata, inda suka mika shi ga rundunar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
DSP Sylvester Anigbogu, jami’in ‘yan sanda na Egume, ya ki cewa komai game da lamarin, yana mai cewa bai da ikon yin magana kan batun.
Duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, ASP Williams Ayah kan lamarin a daren jiya, abun ya ci tura.