By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis a unguwar Mokola dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo yayin da wasu biyar suka samu raunuka daban-daban a wani hatsarin daya rutsa da wata babbar mota dakon iskar gas da kuma wata mota mai wucewa.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Oyo, Uche Chukwurah, wacce ta tabbatar wa da manema labarai faruwar hatsarin tace wata mota ce mai kara kuzari (MDV) ce ta haddasa hatsarin.
Chukwurah tace ta samu labarin cewa motar da hatsarin ya rutsa da ita na dauke da iskar gas ne a lokacin data samu matsala.
Sannan tace: “Mutane biyu ne suka mutu a hatsarin, Na fahimci gazawar birki ce ta haddasa hatsarin. Muna kiran shi (MDV), wanda zai iya zama gazawar lalacewa.sannan Mutane 7 ne lamarin ya rutsa dasu yayin da biyu suka mutu, manya maza biyar da manyan mata biyu.
“Wadanda suka mutu an kai su dakin ajiye gawa na Adeoyo yayin da wadanda suka jikkata yanzu haka suna asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH).”
Wani ganau wanda ya bayyana kansa da Kunle ya shaida wa karidar Aminiya cewa hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da takwas ciki har da wani karamin yaro da ya rasa idanunsa biyu sakamakon hadarin.
Idan dai za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a jiya mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu da da dama suka samu raunuka ciki harda karamin yaron da ya rasa idanun sa biyu.
Sai dai Wani shaidan gani da ido ya bayyanawa wakilinmu cewa motar ta murkushe wadanda lamarin ya rutsa dasu wadanda suka kasance masu safara da kuma wucewa ta yankin.
Ya kara da cewa”Ina wurin, Sun fi biyu da suka mutu a hatsarin. Na ga gawarwaki biyar da kaina, na samu labarin mutane uku suna karkashin motar a lokacin da masu aikin ceto suke ta faman kwashe gawarwakin na bar wajen. Allah Ya jikan su,” inji shi.