By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, tace mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wata mota ta afka cikin kogin Ososa dake kan titin Ijebu Ode-Sagamu a jihar Ogun.
Kwamandan sashin, Mista Ahmed Umar, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Ota, yace wani mutum guda ya samu raunuka daban-daban a lamarin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wata babbar motar dakon siminti ta fada a cikin kogin Ososa a ranar Litinin din da ta gabata, inda direban ya mutu nan take.
Umar ya bayyana cewa wata mota kirar Toyota Camry mai lamba MUS 370 GV da Lexus Jeep mai lamba SMK 08 HK ne suka yi hatsarin daya afku da misalin karfe 3.55 na rana.
Kwamandan sashin yace motocin biyu sun yi karo da juna ne a baya wanda ya sa motar dake gaba ta fada cikin kogin.
Sannan ya ce manya maza bakwai ne suka samu hatsarin, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar maza biyu, yayin da daya ya samu raunuka daban-daban.
Kazalika “An ajiye gawarwakin wadanda abin ya shafa a dakin ajiye gawa na Asibitin Jihar, Ijebu-Ode, yayin da wanda ya tsira kuma yana karbar magani a wannan asibiti.
Umar ya zargi wanda ake zargin ya haddasa hatsarin ne da wuce gona da iri wanda ya kai ga karo a tsakanin motocin biyu, sannan yace wata babbar motar daukar kaya ce ta gano motar da ta fado daga cikin kogin Ososa domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa a yankin.
Kwamandan sashin ya shawarci masu ababen hawa dasu guji wuce gona da iri da kuma rage gudu, musamman yayin da suke tunkarar wata gada ko kwana.Ya kuma jajantawa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa dasu, ya kuma umurce su da su tuntubi hukumar ta FRSC Ijebu-ode domin jin karin bayani.