Hukumomi a kasar Japan sun ce a kalla mutane 20 ne kawo yanzu suka ɓace a birnin Atami na kasar sakamakon wata gogewar kasa.
Wata tashar talabijin na kasar ta nuna yadda laka ie ɓuɓɓugowa daga wani tsauni a kudancin Tokyo, lamarin da ya shafe gudaje da dama.
Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce wannan Ibtila’i ya biyo bayan mamakon ruwan sama ne da aka yan kwanaki da suka gabata.
Kuma tuni Firaminista Yoshihide Suga ya bada umarnin kai agajin gaggawa ga yankin.