Wani Jirgin Yakin Sojin Sama na Najeriya ya gigita barayin daji dake fakewa a cikin dajin rugu na Jihar Katsina wanda hakan ya sanya suka ruga domin neman mafaka.
A sabili da wannan gigitawa da Jirgin ya yiwa barayin ya sanya wasu mutane kimanin su 25 da barayin sukayi garkuwa da su, sun samu hanyar kubuta daga hannun barayin a sa’ilinda suka ruga a cikin na kare, domin neman mafaka daga harin Jirgin.
Kamar yadda wasu daga cikin wadanda suka samu nasarar kubuta suka bayyana, barayin sunyi garkuwa da su kimanin watanni 5 da suka gabata, kuma suna tsare da su a cikin daji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Nada Ararume A Matsayin Shugaban Hukumar Sabon Kamfanin NNPC
Wadandasuka samu nasarar kubuta, sun hada da mata da Maza gami da kananan yara.
Kamar yadda suka shaidawa majiyar jaridar Dimokuradiyya, wasu daga cikinsu anyi yunkurin kai kudin fansa domin karbarsu, daga hannun barayin, sai dai sun kashe wasu daga cikin masu kai kudin a Yayinda sauran suka arce a cikin na kare.
Wannan cigaba na zuwa ne a dai-dai lokacinda Jami’an tsaro ke kara baza kaimi wajen yakar Yan ta’addan a maboyarsu dake cikin dazuka.
Idan dai ba’a manta ba Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin Jagorancin Gwamna Aminu Masari ta sanya wasu dokoki a jihar, dake da manufar shawo kai, da kuma dakile harin masu aikata ayyukan ta’addanci a Jihar.