Najeriya ta sami sabbin wadanda suka kamu da cutar Corona guda 226, a cikin jihohi 14 da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda mutane 6 suka mutu.
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ce ta sanar da hakan a shafinta na yanar gizo a safiyar yau Juma’a.
NCDC, ta bayyana adadin masu da cutar da su Kai kimanin guda 20,8630.
Sabbin wadanda suka kamu da cutar guda 226 a ranar Alhamis, hakan yanuna cewa an Sami ragowa daga cikin mutane 251 da Cibiyar ta bayyana a ranar Laraba a kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gudun Mawar da Sanata Uba Sani ya bayar a Fannin Fasahar Zamani
Cibiyar ta ce FCT ta ba da rahoton mutane 73 yayin da Filato ta ke da guda 34.
Sauran sune Legas (25), Gombe (22), Abia (16), Osun (13), Kano (7), Rivers (7), Ekiti (6), Kaduna (6), Oyo (6), Delta (5) ), Edo (3) Jigawa (2), da kuma Nasarawa (1).
Zuwa yanzu, an tabbatar da bullar cutar guda 20,8630 a Nigeria, yayin da aka sallami mutane 19,6326, sannan an samu mutuwar mutane 2,767 a jihohi 36 gami da babban birnin tarayya Abuja.
Comments 1