By Abbas Yakubu Yaura
Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Afirka, a ranar Alhamis, ta ce Najeriya ta samu karuwar kashi 249 cikin 100 na sabbin mace-mace sakamakon cutar COVID-19 kamar yadda alkaluman rahotannin annoba da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa kasa da mutane 25 sun mutu a cikin kwanaki biyar.
Daraktan Cibiyar CDC na Afirka, Dakta John Nkengasong, yayin wani taron manema labarai na zahiri ya kara da cewa, kasashe mambobi 54 na Tarayyar Afirka sun sayo alluran rigakafi miliyan 547, yayin da aka ba da miliyan 326.
Sannan ya ce, “Akwai matsakaicin kashi takwas cikin dari na sabbin mace-mace da aka ruwaito a Afirka.barkewar mace-macen da akasarin kasashen ke samu sun hada da; Najeriya, matsakaicin karuwar kashi 249; Kenya tana da matsakaicin karuwar kashi 215,sai Afirka ta Kudu kashi 34 na matsakaicin karuwa, ya yin da Habasha keda kashi 12 na matsakaicin karuwar.
“Ya zuwa yanzu, kasashe mambobi 54 ne suka sayo alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 547; An ba da allurai miliyan 326, wanda ya yi daidai da kashi 59.7 na yawan wadatar da ake samu a Afirka.
“Kasashe biyar masu zuwa sun ba da mafi yawan alluran rigakafi a Afirka, Maroko na da miliyan 50.6 yayin da Masar keda miliyan 48.7,sai Afirka ta Kudu mai miliyan 28.2,ya yin da Najeriya ta samu miliyan 15.6,sannan kuma wannan shine kawai kashi 38.3 cikin 100 na jimillar kayayyakin da aka samu, da Mozambique mai miliyan 15.5.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Jimillar adadin alurar J & J da aka kai wa kasashe mambobin kungiyar AU 34 ya kai kimanin allurai miliyan 32.5.”
A halin da ake ciki, bayanai daga NCDC sun nuna cewa a kalla mutane 25 ne suka mutu a tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 5 ga Janairu, 2022.
Ya zuwa ranar 1 ga watan Janairu, 2022, kasar ta ba da rahoton mutuwar mutane 3,033, yayin da cibiyar ta ce adadin wadanda suka mutu a ranar 5 ga Janairu, 2022 ya kai 3,058, wanda ke wakiltar sabbin mutuwar 25.
NCDC, a cikin sabon kundin adireshin ta, duk da haka, ta shawarci wuraren jama’a, gami da masana’antar sufuri, wuraren addini,wurin kasuwanci da kasuwanni da su tabbatar da da bin matakan kiyaye lafiyar jama’a.