Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa ta yiwa mutane 251 rajista, waɗanda suka kamu da cutar Covid-19, a yayinda mutum biyar suka mutu a dalilin cutar a ranar Laraba, wanda adadin waɗanda suka kamu sakamakon cutar yakai dubu ɗari 208,404.
NCDC ta bayyana haka a shafin ta na yanar gizo a ranar Alhamis da safe.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar, mutane 251 da suka sake kamuwa da cutar, ya nuna akwai ƙaruwar waɗanda suke kamu wa da’ita daga 175 da aka samu a ranar Talata a ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugabannin APC Na Delta Ta Kudu Sun Ki Amincewa Da Taron Mazabun Kananan Hukumomi
Hukumar tace ƙarin sabbin wanda suka kamu da cutar yanzu yakai dubu ɗari 208,404, a yayinda aka yiwa mutane dubu 196,123 magani, aka kuma sallame su a faɗin ƙasar.
Hukumar tayi nuni dacewar, mutane biyar da suka mutu a Nigeria, yanzu yawan su yakai dubu 2,762.
Hukumar ta ƙara dacewa, sabbin mutane 251 da aka samu a ƙasar, da mutuwar mutane biyar 5 an same su ne daga Jahohi 13 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Babban birnin Tarayya Abuja (78), Lagos (46), Kaduna (27), Rivers (21), Imo (16), Edo (13), Delta (12), Plateau (10), Niger (7), Bauchi (6), Kwara (6), Akwa Ibom (4), Benue (3) da Jahar Nasarawa (2), inji Hukumar.
An kuma yiwa mutane Miliyan 3,043,321 gwajin cutar, daga cikin mutane miliyan 200 na yawan Al’ummar ƙasar.
Comments 1