Rahotanni sun ce mutane uku ne suka mutu yayin da wasu hudu suka samu raunuka a wani hatsarin da ya rutsa da ayarin motocin Sarkin Mai Tula, Alhaji Abubakar Atare Buba II.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta gano cewa hadarin ya afku ne a ranar Alhamis a kusa da garin Kumo da ke karamar hukumar Akko, a kan hanyar Gombe zuwa Yola.
Lamarin ya kuma yi sanadin mutuwar direban Sarkin Mai Tula, Mai suna Danjuma Mohammed, babban mai kula da dafa abinci, Mohammed Lawal da Adamu Ibrahim, dan sandan da ke aiki tare da tawagar sarkin.
Shaidu sun bayyana cewa, nan take mai dafa abinci da direban suka mutu a yayin da wata mota kirar J5 Peugeot ta bi ta kan wata babbar mota, inda ta rasa yadda za ta yi, sannan ta afka wa ayarin motocin sarkin, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa garin Tula da ke karamar hukumar Kaltungo.
Dan sandan ya rasu jiya a asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe sakamakon raunukan da ya samu.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa wasu mutane uku da suka samu raunuka daban-daban na ci gaba da karbar magani a FTH, Gombe; yayin da aka sallami na hudun.
Da yake zantawa da manema labarai kan lamarin, Atare II ya bayyana rasuwar mutanen uku a matsayin babban rashi ga iyalan gidan sarautar tare da addu’ar Allah ya ba wadanda suka Sami raunika lafiya.
Da aka tuntubi jami’ar ilimantar da jama’a na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) shiyar jihar Gombe, Janet Kassa, ta ce, bata da labarin faruwar lamarin.