By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane hudu ne suka mutu yayin da wasu 6 suka jikkata a wani hatsarin daya rutsa da wasu motocin kasuwanci uku a hanyar Sokoto zuwa Illela.
Mummunan hatsarin ya afku ne a ranar Lahadin data gabata a wani shingen gudanar da binciken jami’an hukumar kwastam ta Najeriya dake Asara, a kan iyakar Illela ta jihar Sakkwato.
A fusace da hasarar rayuka da aka yi, ’yan bangar sun kona motoci biyu mallakar hukumar NCS, wadanda ake zargin jami’ansu da haddasa hatsarin.
Wani ganau wanda ya shaida wa wakilin Jaridar Dimokuradiyya faruwar lamarin, ya ce wata mota kirar Toyota Avensis da wata mota kirar Golf saloon ne suka yi karo da juna a lokacin da suke kokarin gujewa jami’an hukumar ta Kwastam, wadanda ke aikin binciken ababen hawa a shingen binciken.
Daya daga cikin direbobin da lamarin ya shafa, wata majiya ta yi zargin yana jigilar haramtattun kayayyaki da suka hada da shinkafa da man kayan abinci, kuma yana kokarin gujewa kamashi.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Daya daga cikin direbobin da ake zargin yana jigilar shinkafa da man kayan abinci daga iyakar Illela, a kokarin da suke yi na kaucewa kama su, ya shiga wani shingen binciken kwastam da ke kauyen Asara.
“Jami’an hukumar ta Kwastam sun hana direban ne a wani yunkuri na tsayar da motar domin gudanar da bincike wanda hakan ya sa direban ya rasa iko. Motar ta yi karo ne da wata motar da ke tafe sannan wasu motocin da suka taho daga baya suka yi karo dasu biyun.
“Mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu nan take a cikin motoci biyu, yayin da mutane akalla shida suka samu raunuka daban-daban a hatsarin.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Gwandabawa domin kula da lafiyarsu.”
Lamarin a cewar wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya fusata mutanen kauyen da ke kusa, inda suka kona motoci biyu na hukumar ta NCS.
“An dauki matakin cikin gaggawa inda aka aike da jami’an Sojojin Najeriya zuwa wurin domin dakile kai hare-hare kan cibiyoyin Kwastam a yankin,” in ji ganau din.
Wani jami’in Hukumar NCS reshen Jihar Sakkwato da ya zanta da wakilinmu, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Jami’in wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi damar yin magana da manema labarai, ya kara da cewa ’yan dabar sun kona motoci biyu na Hukumar ta Kwastam.
“Jami’an na gudanar da ayyukansu ne kawai ta hanyar hana shigo da haramtattun kayayyaki cikin kasar nan kamar yadda wasu dokoki suka tanada. Abin takaici ne yadda ’yan daba suka kai musu hari,” inji shi.