Mutane biyar sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a garin Mubi da ke arewacin jihar Adamawa.
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta fara ne a gidan mai da sanyin safiyar yau Laraba, lokacin da ake sauke mai daga tankar man fetur kai tsaye zuwa daruruwan jarkoki a Kasuwan Gyela.
Mubi, gari ne na kasuwanci, cibiya ce ta masu fasa -kwauri da ke jigilar jarkokin man fetur cikin dare zuwa kasar Kamaru.
Wani mazaunin garin, Habu Garba, ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, akalla mutane biyar sun kone kurmus sakamakon gobarar yayin da da dama suka samu raunuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Yana ganawa da Goodwill Obasaki
Wani ma’aikacin Hukumar bada agajin gaggawa, Adamu Madobi, ya ce, ya halarci jana’izar wasu ‘yan uwa uku da suka mutu a lamarin.
Madobi ya kara da cewa, sama da Keke Napep 50 da aka ajiye a kusa da gidan man sun lalace a sanadiyar gobarar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADDEMA), Dakta Muhammad Sulaiman, ya ce, mutane uku sun mutu yayin da wasu biyu ke karbar magani a asibiti.
Comments 1