An bayyana cewa mutane shida sun jikkata a ranar Talata da yamma a wani hatsarin mota da ya rutsa da wata motar bas kirar Nissan Vanette a jihar Osun.
A cewar hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC reshen jihar Osun, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 2:15 na rana, kilomita daya zuwa garin Olode, akan babbar hanyar Ife zuwa Olode.
Hadarin dai ya faru ne sakamakon gudun wuce kima da rireban keyi da kuma fashewar taya.
Motar kirar Nissan Vanette mai lamba FFA 433 XB ta yi jigilar fasinjoji akalla 15, yayin da daga cikinsu goma sha uku manyan maza ne, sauran biyun kuma manyan mata ne.
Fasinjojin shida, wadanda aka bayyana cewa, sun samu raunuka daban-daban, sanadiyar Hadarin, akwai maza hudu, da mata biyu.
Kakakin sashin, Agnes Ogungbemi ta bayyanawa Jaridar DAILY POST cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti mai zaman kansa dake garin Olode, domin yi musu magani.