By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane shida ne suka mutu tare da jikkatar wasu 16 a wani hatsarin mota ranar Laraba 9 ga watan Maris a Auchi, hedkwatar karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar Edo.
Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a yayin da wata babbar mota da ke jigilar siminti wanda direban ta ya rasa ikon sarrafa ta inda ta kutsa ta cikin wasu shaguna da dama a cikin al’umma.
Wani ganau mai suna Sani Aliu ya shaida wa jaridar The Nation ta wayar tarho cewa motar na gangarowa daga wani tsauni ne sai birkin ta ya samu matsala inda taci karo da shaguna, tare da lalata kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira.
Aliu ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitocin garin na Kwalejin fasaha da kewaye, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa da ba a bayyana ba.
Sai dai kuma ba a samu jin ta bakin kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) Henry Benamaisia ba a lokacin da ake hada wannan labarin, amma wani babban jami’in hukumar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hukumar FRSC a Ogun ta ce mutane uku ne suka mutu a daren ranar Talata a wani hatsarin da ya faru a unguwar Gofamint da ke Ogunmakin a kan hanyar Legas zuwa Ibadan.mutum daya ya jikkata.
Mista Ahmed Umar, Kwamandan sashin ne ya tabbatar da faruwar hatsarin.