Rahotanni sun bayyama cew mutane shida sun mutu a wani kogi bayan da jirgin ruwan da suke tafiya a ciki ya kife a kusa da kauyen Fada da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP. Catherine Anene, ta fada a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne da karfe 1:00 na ranar Talata.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Kakakin ta ce, jirgin ruwan da ya rutsa da su yana jigilar mutane 40 daga karamar hukumar Guma zuwa karamar hukumar Buruku domin gudanar da harkokin kasuwanci a yayin da ya kife a kusa da kauyen Fada da ke Guma.
KARANTA KUMA: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutane 15
“Yan sanda tare da hadin gwiwar masunta a yankin ya kai ga ceto mutane 26 da aka kai asibiti domin yi musu magani, an gano gawarwaki shida (6) yayin da ake neman sauran mutane takwas (8) da har yanzu ba a gansu ba.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Benue, CP. Wale Abass, ya jajantawa iyalai da abokan mamatan yayin da yake ba da shawara ga matafiya da suka zabi jigilar ta ruwa da su yi amfani da mafi girman matakan tsaro yayin tafiya kan ruwa musamman a yanzu da ruwa ya yi yawa, ”in ji Anene.
A wani labarin kuma: ‘Yan Rasha 10,000 Sun Bukaci A Turasu Yaki A Ukraine
Bayan sanarwar da Rasha ta fitar a jiya na cewa za ta tura dubunnan dakaru domin yaki a Ukraine, kakakin rundunar sojin Rasha ya ce tuni ‘yan kasar Rasha 10,000 suka ba da kansu da kansu a ranar farko ta fara yada wannan gangamin. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
“Kimanin ‘yan kasar 10,000 ne suka isa ofisoshin daukar Jami’an soji da kansu ba tare da jiran an kira su ba,” in ji Vladimir Tsimlyansky a cikin kalaman da kamfanin dillancin labaran Rasha Interfax ya nakalto.