Akalla mutane 650 ne suka samu gwajin cutar HIV/AIDs da zazzabin typhoid da ciwon suga da idanu da sauran cututtuka kyauta a karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Mamba mai wakiltar mazabar Lafia/Obi, Abubakar Sarki-Dahiru ne ya dauki nauyin aikin kyauta ga al’umar mazabarsa, da aka kwashe tsawon kwanaki uku a na gudanar da shi a yankin.
Da yake jawabi a ranar Lahadin da ta gabata, Sarki-Dahiru ya bayyana cewa dalilin shirin shi ne don baiwa wadanda suka ci gajiyar tallafin damar sanin halin da suke ciki, domin hana yaduwa Cututtuka a cikin al’uma, tare da kuma tallafa musu.