Rahotanni na nuna cewa mutane hudu sun mutu har lahira yayin da wasu biyu suka bace bat, lokacin da motar fasinja ta afka cikin Kogin Niger, a yankin Koton Karfe na jihar Kogi.
Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC ta hannun Solomon Agure, kwamandan sashinta na jihar, ya tabbatar da wannan mummunan lamari, a cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Laraba a garin Lokoja babban birnin jihar.
A cewar hukumar ta FRSC, wata mota kirar Toyota Hiace dauke da fasinjoji 15, ta fada cikin kogin ne da yammacin jiya Talata.
Hukumar ta ce, Bas din mai lamba jihar Filato – JJN 73 XA, ta taso ne daga Ijora Seven Up, karkashin gadar Legas, inda kuma za ta nufi jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani hari ya hallaka Yan kungiyar Taliban 2 a Jalalabad
A cewar Agure, mutane hudu sun mutu a hadarin, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka.
Ya Kara da cewa,, hukumar ta tura jami’an da su ka kware a cikin ruwa domin ceto wadanda abin ya rutsa da su, inda nan take aka gano gawarwaki hudu.
Agure ya bayyana cewa fasinjoji biyu mata sun bace bat, inda Kuma ya kara da cewa, duk kokarin da hukumar ta wurinyi gano gawarwakin nasu abun ya ci tura.
Kazalika ya bayyana cewa, fasinjoji biyu sun tsira da rayuwarsu, ba tare da sun ji rauni ba.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom yace Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari taki taimaka masa ya kawar da wasu matsaloli na biyan kudade, sabudda kawai yana fadin gaskiya.
Ortom ya bayyana cewa, akwai wadanda suka same shi daga Jami’iyyar APC mai mulki, inda suka ce taimako zai zo ne Jahar Benue idan shi ya koma Jami’iyyar.
Gwamnan yace bashi da ra’ayin sayar da Al’ummar sa, kamar yadda wasu Gwamnoni suke yi a yanzu, inda yace zai cigaba da jajircewa akan su.
Ortom ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta Daily Post, akan yadda ya samu nasarar shimfida ayyuka masu yawa da kudin da Gwamnatin sa ke samu.
A cewar Gwamnan “Ina godewa Allah, duk da anyi mani wulakanci, an bata mani suna da sauran abubuwa. Amma ni ina son kasar nan ta samu cigaba.
“Nayi imani da kasa ta Nigeria, wannan ne ya sanya nake dauke da kalar Nigeria, kuma kalar manyan kabilu na Kasa a Benue kamar su; Tiv, da Idoma, da Egede.
“To nayi Imani akan Nigeria daya. Hadin kai muke so kuma bama son rabuwa. Karfin mu shine hadin kai. Kuma nayi Imani mutanen mu zasu kasance akan haka.
“Wani abu dana rike shine nayi rantsuwar kama aiki da littafina na Bible, kamar yadda Shugaban Kasa yayi rantsuwar kama aiki da Al-kur’ani, to abinda nayi imani shine fadin gaskiya a kowane lokaci.
“A kowane lokaci dole zamu kare kundin tsarin Mulkin Nigeria. Wannan shine na tsaya akanshi, kuma zamu cigaba da yaki akan dai-dai to, da gaskiya da adalci.
“Gwamnatin Tarayya taki taimaka mani wajen tabbatar da biyan kudaden ariyas na Fansho da garatuti Wanda na gada, ba laifi na bane. Aper Aku yana da alhakin biyan kudaden ariyas na Fansho da garatuti, Akume yana da hakan, Adasu na dashi, Suswan yana dashi, Na gaji biyan Naira biliyan 70 na kudaden ariyas na Fansho da garatuti da zan biya, don haka wannan sabon abu bane.
“Gwamnatin Tarayya ta bani Biliyan 28 amma bata isheni ba. An ba wasu Karin kudade, amma sabudda ina fadin gaskiya, sun ki bani kudi.
Gwamna Ortom wanda ya lashe kujerar Gwamna a karkashin inuwar Jami’iyyar APC, ya bar Jami’iyyar gabanin Babban zabe na Shekarar 2019, inda ya samu nasarar lashe wa’adi na biyu a karkashin Jami’iyyar PDP.
Comments 1