By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kashe gobara ta tarayya FFS ta bayyana yadda ta rage mace-macen dake da alaka da aukuwar tashin gobara, inda ta ce a shekarar 2021, an yi asarar rayuka 70 sabanin mutuwar mutane 147 da aka samu a shekarar da ta gabata.
Hakan ya faru ne yayin data bayyana yadda ta ceci kadarorin da suka kai kimanin Naira Tiriliyan 19.4 a shekarar 2021, inda ya yabawa ‘yan Najeriya da kuma ‘yan uwan jami’an tsaro kan hadin kan da suke bayarwa.
Shugaban hukumar kashe gobara ta kasa, Dakta Ibrahim Alhaji Liman ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ugo Huan.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa a yanzu hukumar ta fi dacewa da daukar matakin daya dace kan aukuwar gobara da sauran abubuwan gaggawa.
Sannan ya ce: “Idan ka duba alkaluman kashe gobara a bana idan aka kwatanta da sauran shekaru, za ka ga a bana an samu raguwar asarar rayuka daga mutane 147 a shekarar 2020 zuwa 70 a shekarar da muke bankwana da ita ta 2021 da kuma karuwar kiyasin dukiyar da aka ceto. Daga Naira Tiriliyan 1.4 a shekarar 2020 zuwa Naira Tiriliyan 19.4 a shekarar 2021”.
Liman ya kara da cewa kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya ya sa aka siyo kayayyaki na kashe gobara da horar da ma’aikatan hukumar.
Kazalika ya bayyana cewa kafin shekarar 2015 hukumar kashe gobara ta tarayya tana da manyan motocin kashe gobara guda uku ne kacal, amma yanzu hukumar ta sayo motocin kashe gobara na zamani guda 141, karfin ma’aikata ya karu daga 600 zuwa sama da 6,000, sannan hukumar ta fadada ayyukan ta a dai dai lokacin, Jihar Legas da Abuja, zuwa dukkan jihohin tarayya.