A aƙalla mutane takwas ne suka ƙone a wani haɗarin mota da ya ritsa da su akan babban titin Legas zuwa Ibadan.
Haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 8:30 ma dare kusa da gadar Saapade da wata mota ƙirar Bas mai ɗauke da lamba kamar haka AAA 249 VX.
Jami’in hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa Ahmed Umar ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.
Umar ya ƙara da cewa haɗarin ya rista da mutane 11 ne amma takwas daga ciki sun ƙone ƙurmus har lahira sakamakon tuƙin ganganci da wani mai mota ya musu, wanda hakan ya jawo fashewar tayar motar.
Ragowar wanda suka tsallake rijiya da baya an garzaya dasu asibiti domin basu agajin gaggawa.
Umar ya ja hankalin masu ababen hawa da su dinga kula da kuma bin ƙa’idojin tuƙi domin kiyaye faruwar irin hakan a nan gaba.