By Ishaq Dabai
Biyo bayan sabbin bayanai da Cibiyar dakile yaduwar Cututtuka ta Nigeria (NCDC) ta yi, an samu sabbin mutuwar mutane takwas wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu a kasar zuwa 2,731.
Hukumar NCDC ta tattara sabbin wadanda suka ka kamu da cutar guda 344 a jiya Talata.
Bayanan NCDC ya nuna cewa, Babban Birnin Tarayya Abuja ta sami adadi mafi yawa guda 75, jihar Legas ta sami guda 63, sannan jihar Ribas ta samu 45.
Jihar Kaduna ta samu mutane 33, sai Filato da ke biye da mutum 22; Edo, 16; Benue, 13: Kano, 12; yayin da jihohin Cross River da Delta suka Sami mutane 11 kowannensu.
Hakanan, Anambra da Abia sun sami tara da takwas bi da bi, Jigawa na biye mata da masu cutar guda bakwai.
Jihohin Bauchi, Ekiti da Kwara sun samu mutane guda hudu kowanne su, jihar Oyo ta samu biyu, yayin da Akwa Ibom da Nasarawa suka Sami daya kowannensu.
Comments 1