Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC reshen jihar Ekiti, Mista Olusola Joseph, ya bayyana a ranar Alhamis din nan cewa, mutuwarsu ta biyo bayan wani karo da wata motar bas mai dauke da mutane 18 da wata mota kirar Toyota.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a daidai lokacin da direban daya daga cikin motocin ke kokarin kaucewa wani rami a kan hanyar.
Karanta kuma: Gwamnatin Ekiti Ta Rusa Majalisar Gudanarwa Ta Jami’ar BOUEST A Jihar
“Direban daya daga cikin motocin da abin ya shafa yana kokarin taka wani rami ne kafin ya rasa yadda zai yi, sannan ya yi karo da daya motar.
Kwamandan sashen ya ce an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa.
“Wadanda suka samu raunuka daban-daban suna karbar magani a asibitin Afe Babalola Multi System Hospital da ke Ado Ekiti,” inji shi.
Jaridar Vanguard ta rawaito Joseph ya gargadi masu ababen hawa kan wuce gona da iri inda ya dora alhakin faruwar hatsarin a kan rashin bin ka’idojin ababen hawa.
A wani labarin kuma: Kwankwaso Ya Ci Amanata– Inji Shekarau
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya ce Sanata Rabiu Musa ya ci amanar shi da mabiyansa, inda ya ce dalilin da ya sa suka fice daga jam’iyyar ke nan.
Shekarau ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today.