By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 5 ne ake fargabar an kashe su a Igbokoda, hedkwatar karamar hukumar Ilaje, biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin asiri.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Majiyoyi sun ce rikicin kungiyar asiri kan rikicin filaye a yankin ya yi sanadiyar mutuwar alkalla sama da mutane 20 tun daga watan Mayun bana zuwa yanzu.
Daga cikin wadanda aka kashe a cikin kwanaki ukun da suka gabata akwai wani mashahurin Disc Jockey a yankin da wani mai tuka babur mai kafa uku Idowu Agbude da kuma wani mazaunin garin Asogbon Obayomi.
Wani dan kabilar Igbokoda, Prince Emorioloye Owolemi, ya ce rikicin kungiyar asiri ya faro asali ne tun a shekarar 2012.
Shugaban karamar hukumar, Olamogoke Jatuwase, yace an hada jami’an tsaro domin kwantar da hankula yankin.
“Na ziyarci Akure, babban birnin jihar domin kai rahoto ga gwamnatin jihar kuma na yi imanin suna samar da mafita mai dorewa kan lamarin.”
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Ondo, Fumilayo Odunlami, mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda (DSP), tace har yanzu ba a yi mata karin bayani kan faruwar lamarin ba.