By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi Allah-wadai da sabbin kashe-kashen da aka yi a kan iyakar kananan hukumomin Kauru da Zango-Kataf na jihar inda aka ce an kashe wani makiyayi a ranar Talata.
An tattaro cewa makiyayin na kiwo a kusa da yankin ne lamarin ya faru biyo bayan kaurewar gardama da wani manomi.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Sanarwar mai taken, ‘Kaduna ta yi Allah-wadai da sake kashe-kashen da aka yi a yankin Kauru zuwa Zangon Kataf.’
Aruwan ya ce makiyayin mai suna Yusuf Mahmuda, wanda shi ma mazaunin unguwar ne, an fille kansa yayin da sauran makiyayan suka tsere daga yankunan.
Fille kan makiyayin, ya ce ya haifar da rikicin kabilanci da ya barke a Kasuwar Bakin Kogi ta Kauru, wanda ya yi sanadin kashe Ahmad Aliyu guda daya, yayin da wasu mazauna garin Esther Thomas da Tanko Dakar suka jikkata tare da bankwa wata mota wuta.
Kwamishinan, ya ce sojojin na Operation Safe Haven ne suka shawo kan lamarin dan kwantar da hankula.
Aruwan ya ce, “Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da sabbin kashe-kashen da aka yi a yankunan kan iyakar Kauru da Karamar Hukumar Zangon Kataf kamar yadda hukumomin tsaro suka ruwaito a wadannan wuraren.
“Gwamnati ta yi kira ga mazauna yankin da suka rasa ‘yan uwansu da su baiwa jami’an tsaro da gwamnati damar gudanar da lamarin, saboda ana ci gaba da gudanar da bincike, biyo bayan faruwar lamarin da ya haifar da tashin hankali a kananan hukumomin.
“A cewar rahoton, makiyayin, Yusuf Mahmuda, mazaunin unguwar, yana kiwo tare da wasu makiyaya a cikin dazuzzukan da ke daura da wasu gonaki, inda aka kai masa hari aka kashe shi bayan gardama da wasu manoma kan satar dabbobi.
“Bayan haka, rikicin kabilanci ya barke a lokacin da kasuwar ta tashi a kasuwar Bakin Kogi ta karamar hukumar Kauru da ke kusa da iyakarta da karamar hukumar Zangon Kataf.
“An kashe Ahmad Aliyu daya a harin, yayin da wasu mazauna garin Esther Thomas da Tanko Dakar suka samu raunuka tare da kona wata mota. Dakarun Operation Safe Haven ne suka shawo kan lamarin, inda suka raka masu saye da masu siyarwa zuwa wurin tsira.”
Ya kara da cewa, “Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana bakin cikinsa kan rahotannin, ya kuma koka da yadda hare-hare da fadace-fadacen da suka barke a yankin gaba daya.
“Ya nuna matukar damuwarsa cewa duk da kokarin da gwamnati da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suke yi don ganin an dawo da zaman lafiya sannu a hankali, kashe-kashen ya haifar da koma baya wanda kuma bai kamata a bari a samu nasara ba.
“Ya jajanta wa iyalan wadanda aka kashe, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan su, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
“Gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan hare-haren da suka kai ga asarar rayuka a wurare biyu. Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu.
“Hukumomin tsaro suna binciken abubuwan da suka faru tare da ci gaba da sintiri don dawo da kwanciyar hankali a yankin gaba daya.”