A kalla mutane biyu ne ake kyautata zaton sun mutu bayan da ambaliyar ruwa ta yi awun gaba da motarsu a kauyen Malka dake karamar hukumar Ningi a Jihar Bauchi.
Ambaliyar ruwa da ta biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana shekawa, ta yi sanadiyar ruftawar gadar da ta haɗa Bauchi zuwa Ningi zuwa Kano da kuma Jigawa.
Sai dai an yi nasarar ceto wasu fasinjoji dake cikin motar da ambaliyar ta wuce da ita , yayin sa aka garzaya da su asibiti nan take.
Wakilin mu a Bauchi Bashir Khalid Furyam ya labarto mana cewa jama’a da dama ne suka makale a hanyar ta Bauchi zuwa Ningi zuwa Kano, sakamakon karyewar gadar da babu halin wucewa.
Wani mazaunin kauyen ya shaida mana cewa wata tirela dauke dabbobi da suka hada da shanu da awaki da tumaki na daga ciki wanda ambaliyar ta ritsa da su, inda dabbobi sama 200 suka mutu nan take.
Kuma tuni Kakakin Majalisar dokokin jihar Abubakar Suleiman wanda ke wakiltar yankin, halarci inda lamarin ya faru don ganewa idanunsa irin ta’adi da ambaliyar ta yi.
A bangaren shugaban karamar hukumar Ningi Alhaji Mamuda Tabla ya ce sun samu bayanan shafewar gidaje sama da ashirin duk a ranar ta juma’a.