Akalla mutane biyu ne aka kashe a yammacin ranar Talata a kauyen Ancha da ke gundumar Miango a masarautar Irigwe na karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Malison, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Cigaban al’umar Irigwe ta kasa (IDA), ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an yi wa wadanda suka mutu kwanton bauna ne a gonakinsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya kara da cewa an baza jami’an ‘yan sanda zuwa inda harin ya faru.
Malison, wanda ya bayyana sunayen mamatan da Daniel James Mai shekaru (32) da Zakwe Deba Mai shekaru (35), ya ce: “Na yi magana da DPO Bassa kan lamarin wanda ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa wurin.
“Dukkan al’ummar Rigwe na cikin bakin ciki da wannan mummunan lamari da aka samu tare da yin kira da a kara daukar matakai daga jami’an tsaro da gwamnati wajen kawo karshen wannan zubar da jini a kasar”
Ya kara da cewa, “Wadannan ta’asa da ‘yan ta’addan Fulani ke aikatawa sun yi mummunar illa ga jama’ar mu, don haka dole ne a dakatar da su.”
Kakakin ya zargi Fulani makiyaya da kai harin.
Sai dai shugaban kungiyar Fulani ta Gan Allah ta Najeriya (GAFDAN), Malam Garba Abdullahi, ya musanta zargin, yana mai cewa; “zargin ba shi da tushe balle makama.
“Mutanenmu ba sa kiwon shanu a masarautar Irigwe” inji shi.
Comments 2