Mutane da dama a Najeriya sun yi alawadai da sabon ƙarin farashin man fetur zuwa N143.80 da gwamnatin tarayya ta yi.
Sanarwar da aka fitar ranar Laraba ta nuna yanzu za a rika sayar da litar man ne a kan sabon farashin, sabanin Naira 123.50 da aka saba sayarwa a baya.
Karin dai na zuwa ne a ranar da aka dage dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi a fadin Najeriya.
https://dimokuradiyya.com.ng/farashin-man-fetur-ya-koma-143-80/
Sanarwar Hukumar da ke ke kula da Kayyade Farashin Albarkatun Mai ta Kasa (PPPRA), ta ce karin ya zama wajibi la’akari da kudaden da ‘yan kasuwa ke kashewa wajen dakon man da kuma isar da shi zuwa jihohi.
Rahotanni dai sun nuna cewa zuwa ranar Laraba, farashin danyen mai ya kan kai Dala 39.81 a kan kowace ganga.
To amma mutane da dama a faɗin ƙasar nan sun bayyana rashin jin dadinsu da wannan ƙari da aka yi saboda suna ganin wannnan ba komai bane face zalunci da kuma ƙuntatawa.
Hakan ya jawo wasu wallafa ƙorafe-ƙorafe a kafafofin sada zumunta, wajen kira ga gwamnatin tarayya da ta sake yin duba ga wannan sabon mataki da ta ɗauka.