Akalla mutane 20 da suka hada da mata da kananan yara ne suka nutse a kogin Guni-Zumba a lokacin da suke gudun hijira sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai musu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun tsere ne lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan Guni da Kurgbaku da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba lokacin da ‘yan bindiga suka mamaye al’ummun biyu, lamarin da ya tilastawa mutanen yankin tserewa.
Majiyoyi sun ce, wadanda lamarin ya rutsa da su na tsallakawa kogin zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Zumba da Gwada ta cikin kwale-kwalen.
Wani mazaunin garin Shehu Abubakar ya shaida mana cewa jirgin na dauke da kayan da yafi karfin shi ne, wanda hakan ya sa ya kife a tsakiyar ruwa.
“Yan bindiga sun mamaye al’ummarmu da safiyar yau, kuma a kokarin guduwa wasu mutane sun nutse a kogin Guni-Zumba. Sakamakon lodin kaya, kwale-kwalen ya kife a tsakiyar ruwa. Ya zuwa yanzu, ba mu san adadin wadanda suka mutu ba saboda ba mu samu nasarar ceto kowa ba amma zan iya fada muku cewa sama da mutane 20 ne suka hada da mata da yara a cikin ruwan..”
Kazalika Mutum ya Kuma koka da rashin tsaro a yankin.
Wani mazaunin garin, Mai suna Michael Madaki, ya ce, “’yan bindiga sun kai hari a kauyen Guni da ke karamar hukumar Munya ta Jihar Neja, mutanen kauyen suna kokarin tserewa amma kwale-kwalen da suke ciki ya kife.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran da aka yi masa ba da kuma sakon da aka aike masa.