Wakilinmu shu’aibu Ibrahim Gusau
Kimanin mutane Dubu 6268 zasu amfana daga tallafin Gwamnatin tarayya wadanda suka gamu da annobar ambaliya a shekarar 2017 zuwa 2018, da ta Gabata.
Babban sakatare na hukumar bada tallafi na jihar zamfara, injiniya Sanusi kwatarkwashi, ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabinsa wurin bukin kaddamar da kayan tallafin a jihar Zamfara.
Ya kara da cewa tallafin ya kunshi irin masara da magani da irin dawa da taki da Goran Feshi da dai sauransu, su dai wadannan kayan Noman maza ne kawai za’a baiwa, Kuma kimanin mutane Dubu 4140 ne zasu amfana da kayan Noman.
Su kuwa masu kiwon Awaki, mutun 989 sune za’a baiwa Awaki guda uku mata biyu sai Busuru guda, su kuwa masu kiwon kaji su 1139.
Ya ce duka Adadin wadannan mutanen zasu fitone daga kananan hukumomi guda shida, Wanda ya kunshi Bungudu, da Maru, da Gusau, Da Kuma kauran Namoda, sai Karamar hukumar Tsafe, daTalatar mafara.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin Malama Aisha Shu’aibu, ta bayyana cewa tayi matukar farin ciki Kuma tana Rokon Allah ya Sanya Albarka cikin abinda zata kiwata.