Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutane 700,000 ne ke kashe kansu a duk shekara a fadin duniya.
Ta kara da cewa kashi 77 cikin 100 na kashe-kashen da ake yi a duniya na faruwa ne a kasashe masu karamin karfi da matsakaita.
Dr Walter Mulombo, Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Najeriya ne ya bayyana hakan a cikin sakon tunawa da ranar yaki da kashe kai ta duniya ta shekarar 2022.
KARANTA ANAN: Yanzu an wuce zamanin Magudin zabe – INEC
Mulombo ya ce ranar da ake bikin ranar 10 ga watan Satumba na kowace shekara, an yi ta ne da nufin wayar da kan jama’a da ake bukata cewa ana iya kare kai.
“Ga kowane wanda ya kashe kansa, akwai yiwuwar wasu mutane 20 da ke yin yunƙurin kashe kansu kuma da yawa suna da tunanin kashe kansu.
“Kisan kai shi ne na hudu da ke haddasa mace-mace tsakanin mutane masu shekaru 15 zuwa 29,” in ji shi.
A cewarsa, taken ranar ta bana shine “Samar da bege ta hanyar aiki tukur” wanda ke zama abin tunatarwa cewa akwai madadin kashe kai.
Ya ce hanya ta musamman kan yaki da wannan dabi’a shine, zuwa wajen likitan ƙwaƙwalwa domin sanin halin da kwakwalwar mutum ciki.
A cewarsu hakan zai taimaka wajen kawo karshen kashe kai da ake yawan samu.
A wani labarin kuma: Sarauniya Elizabeth II: Buhari ya bada umarnin sausauto da Tutocin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sausauto da dukkanin tutoci a ƙasar nan da ofisoshin jakadanci na ƙasashen Ƙetare a ranakun 11 da 12 ga watan Satumba domin girmama rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu.