Akalla sama da mutum goma sha biyu suka kamu da cutar Ebola a kasar Dimokuradiyyar Congo, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta tabbatar a ranar Litinin
A makon da ya gabata, hukumomi a kasar sun tabbatar da cewa an samu mutum shida da suka kamu da cutar a arewa maso yammacin birnin Mbandaka, inda suka ce wannan daban ne da wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullarsa a cikin shekarar 2018.
Ya zuwa yazu an sake tabbatar da kamuwar mutum Tara, da kuma wadansu guda uku na daban wanda cutar ta kama a birnin Mbandaka inji WHO.
Sai WHO din sun ce mutum shida daga cikin su rasa ransu sakamakon cutar. Birnin na Mbandaka yana kusa da kogin Congo, kusa da iyakar Jamhuriyyar Congo.