By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane hudu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yammacin ranar Lahadi a kusa da Giwo Science Academy, a kan hanyar Bauchi zuwa Kano, kimanin kilomita 10 daga cikin birnin Bauchi.
Wasu mutane bakwai sun samu raunuka daban-daban a hatsarin wanda ya hada da wasu motocin kasuwanci guda biyu kuma ya faru ne sakamakon wuce gona da iri da kuma tukin ganganci.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar wa wakilinmu afkuwar lamarin ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 2:45 na rana.
Ya ce motocin da lamarin ya shafa guda biyu kirar Sharon bas mai lamba, TRR391YX da kuma Opel Vectra Salon mai lamba: AA268 SHR.
Abdullahi ya ce har yanzu ba a iya tantance sunayen direbobin motocin biyu ba.
Ya ce, “Eh, an yi hatsari a kusa da Giwo Science Academy, a kan hanyar Bauchi zuwa Kano. Lokacin da aka kira mu, mutanenmu sun garzaya zuwa wurin cikin mintuna 10 don ceto.
“Hatsarin wanda ya faru ne ta hanyar keta haddin gudu da kuma tuki mai hatsari, ya hada da motoci biyu, wata motar bas Sharon mai lamba: TRR391YX da kuma Opel Vectra Salon mai lamba: AA268 SHR.
“Mutane 17 ne da suka hada da manya maza tara, manya mata hudu da kuma yarinya mace daya.
“Mutanenmu sun garzaya da su Asibitin Kwararru da ke Bauchi don duba lafiyarsu, inda wani likita ya tabbatar da mutuwar mutane hudu, manyan maza uku da mace guda daya.
“Wadanda suka samu raunuka daban-daban manya ne maza biyar da mata biyu manya.
Sannan yace “An ajiye gawarwakin nasu a asibiti guda inda za a mika su ga ‘yan uwansu don yi musu jana’iza.”