Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Benue Yakubu Mohammed ya tabbatar da mutuwar mutane hudu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.
Mohammed ya ce hatsarin ya afku ne ranar Alhamis a Makurdi da karfe 11:48 na safe a kusa da sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) Orientation Camp, na Wannnune, a karamar hukumar Tarka ta jihar.
Ya ce mutane 15 ne suka jikkata a sanadiyar afkuwar hatsarin.
Ya ce an kai wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu zuwa Asibitin St. Christopher da kuma Asibitin NKST da ke Wannnune.
“Mota daya kacal lamarin ya rutsa da ita, ita ce wata mota kirar Toyota Hiace wacce ke jigilar mutane 19.
“A cikin adadin mutane 18 mata ne da namiji daya”
“Musabbabin hatsarin shine gudun wuce kima” in ji Mohammed