An tabbatar da mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 3 a wani rikici da ya barke tsakanin mazauna yankin, da wasu makiyaya a Jankasa da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Kwamishinan kula da harkokin cikin gida da al’amuran tsaro na jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Litinin.
Inda ya ce rikicin ya kaure ne a wasu labin kiwon shanu a yankin, kafin daga bisani lamarin ya bazu izuwa tsakanin bangarorin biyu.
Zuwan jami’an tsaro yankin , ya sanya wutar rikicin lafawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari ya Rantsar da Kwamishinonin Hukumar Zabe biyu
“Bayan arangamar, an bayyana sunayen mutane hudu da aka tabbatar sun mutu: Luka Nelson, Timothy Koni, Pasi Peter da kuma George Francis.”
“Mutum uku da suka samu raunuka na harbin bindiga a lokacin rikicin sun hada da: Daniel Dauda, Extra James da Henry Frances. Yanzu haka mutanen da suka jikkata suna karbar magani a wani asibiti.”
Bugu da kari, hukumomin tsaro sun ba da rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kai hari ga wasu makiyaya da ke zaune a Manchok, Karamar Hukumar Kaura.
Sai dai Hukumomin tsaro sun ba da rahoton cewa wannan ramuwar gayya ce ga rikicin farko.
“Ya zuwa yanzu an tabbatar da kashe shanu 13, yayin da sojoji suka kwato shanu 25 da rai, daga yankin”
“Sai dai Kuma ba a ba da rahoton asarar rayuka ba, yayin da ake ci gaba da bincike.”
Kwamishinan ya ce hukumomin tsaro na ci gaba da sintiri a yankunan baki daya, domin tabbatar da doka da Oda.