Wasu mazauna unguwar Ojoo da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun fuskanci harbin da ba a taba gani ba daga wajen rundunar sojojin Najeriya ta biyu da ke Odogbo a Ibadan.
Daily Trust ta ruwaito a ranar Asabar cewa wadanda abin ya shafa dai Daniel ne dan shekara 10, yayin da dayan kuma babba, an bayyana sunansa da Baba Ajeri.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC Ta Kama Masu Damfara Ta Yanar Gizo A Jihar Kwara
Mutanen biyu da abin ya rutsa da su suna karbar magani a wani asibitin bariki da dake jami’an lafiyan sojoji.
Wasu mazauna garin da suka zanta da majiyar Dimokuradiyya a ranar Asabar sun ce an fara harbe-harben ne a ranar Juma’a.
Wani mazaunin garin Mista Olaogun Alade ya ce duk da korafe-korafe da kungiyar mazauna yankin suka yi, har yanzu ana ci gaba da harbe-harbe.
Alade ya ce mazauna garin da dama sun bar gidajensu yayin da da dama ke cikin gida saboda fargabar mutuwa.
Ya tabbatar wa Diaky Trust a ranar Asabar cewa gine-gine, musamman rufin gidaje sun lalace sakamakon harbin bindiga da aka yi a wajen.
Wani jigo a yankin, Alhaji Kareem Ijeru, ya shaida wa manema labarai cewa, sabon harbe-harbe ya yi tsanani a daren Juma’a, kuma jama’a da dama sun ajiye motocinsu a wajen gidajensu.
“Kowa ya zauna a gida kuma dukkanmu mun kwanta don gudun kada harsashi ya same mu a cikin gidajenmu. An ci gaba da harbe-harbe a safiyar yau, kuma abin takaici, an samu mutane biyu.
“An garzaya da su asibiti a bariki. Harsashin da ya same Baba Ajeri ba a cire shi ba, amma Daniel ya yi sa’a, an ce min wanda ya same shi an ciro shi.
“Mun gudanar da zanga-zanga; mun kai karar sojojin a lokuta lamarin ga rundunar soji da dama amma lamarin bai canza ba.”
Da aka tuntubi jami’in yada labarai na runduna ta biyu ta sojojin Najeriya Laftanar Kanar Charles Ekeocha, ya shaida wa Daily Trust ranar Asabar cewa ba ya nan, amma ya yi alkawarin zai sake kira.
A WANI LABARIN KUMA; 2023: NNPP Ta Sha Alwashin Karbe Mulki Daga Hannun Jam’iyyar PDP A Jihar Enugu
Gabanin zaben 2023, jam’iyyar NNPP, ta sha alwashin karbe mulki daga hannun jam’iyyar PDP a jihar Enugu.
Shugaban jam’iyyar na jihar Enugu, Dr. Tony Ngene ya bayyana hakan a yayin wani taron koma-baya na kwana daya/ wayar da kan masu kada kuri’a da aka shirya wa daukacin ‘yan takararsu da shugabannin kananan hukumomi na jam’iyyar.