By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi a ranar Larabar da ta gabata ta tabbatar da mutuwar mutane shida a yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan mazauna garin Bagana dake karamar hukumar Omala ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne da sanyin safiyar ranar Litinin
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Idrisu Dabban, wanda ya ziyarci garin Omala domin tantancewa, yace da alama harin na ramuwar gayya ne na harin da aka kai a watan Agusta wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.
Ya ce, “Mun zo nan ne don yin kira ga jama’a cewa tashin hankali ba ya magance wata matsala;su rungumi tattaunawa wajen warware sabanin dake tsakaninsu.”
Wakilinmu ya bayyana cewa maharan sun je fadar sabon shugaban masu daraja ta uku, Salifu Anyebe, inda suka kona shi tare da harbe mutane uku har lahira, ciki har da wata Madam Achebe Alih wadda aka fi sani da ‘Mama Teacher.Majiyoyi sun ce mutanen kauyen sun shiga cikin daji domin tsira da rayukansu a lokacin da suka kai farmakin da sanyin safiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ramuwar gayya ta kai ga kona fadar Oga Onu Ife, wani babban basarake kuma Hakimin Bagana, Cif Alih Haruna, yayin da kuma aka kona wasu gidaje na wasu manyan mazauna garin.
Kazalika yace tun a shekarar 2013 da rikicin ya barke a tsakanin makiyaya da manoma, “inda ya yi dusar kankara kana ya koma rikicin kabilanci wanda yayi sanadiyyar Mutuwar kimanin mutane 300.
Mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro a karamar hukumar Omala, Steve Shaibu, ya tabbatar da mutuwar mutane shida, inda ya kara da cewa mutum daya ya samu rauni.