‘Yan sa’o’i kadan bayan rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa an yi garkuwa da mutane 20 a kan gadar Kara, da ke kan titin Legas zuwa Ibadan, a ranar Laraba ‘yan fashi da makami sun ‘kwace’ iko da gadar.
Masu laifin sun mamaye doguwar gadar, lamarin da ya sa masu ababen hawa, ’yan kasuwa da mazauna wurin tserewa domin tsira da rayukansu.
An ce barayin sun kwace wa mutane wayoyinsu da kudade da sauran kayayyaki masu daraja ta hanyar tsoratar da su da bindigogi.
Duk da cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin sanya ido na tsawon sa’o’i 24 a kan babbar hanyar, amma shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun yi rana da wuri domin babu mai kalubalantarsu.
Ka gargadi magoya bayan ka – Tinubu ya ja kunnen Peter Obi kan yada labaran karya
A wani labarin kuma na daban.
Hajiya Yar-Sokoto Jega, shugabar mata ta jam’iyyar PDP mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a jihar Kebbi, ta koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Jega ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke jawabi a wajen wani biki a Birnin Kebbi a ranar Laraba.
A cewarta, ta bar jam’iyyar ne saboda rashin adalci da kuma rashin shugabanci na gari.
Jega ta bayyana cewa ta yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne saboda dimbin nasarorin da Gwamna Atiku Bagudu ya samu, inda ta kara da cewa ta koma jam’iyyar ne da magoya baya sama da 800.
“Na shafe shekaru da yawa a PDP, ba su da wani abin da za su nunawa mutane kuma jam’iyyar ta yi watsi da mu.
“Ni ma ina amfani da kudina wajen tafiyar da jam’iyya, amma duk da haka ban ga wani sauyi da jama’ata ta samu ba, musamman matan da nake wakilta.
“Kafin sauya sheka na, ina shugabancin kananan hukumomi takwas a karkashin jam’iyyar PDP, na tafi tare da mafi yawan mabiyana,” in ji Jega.
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da Alhaji Abubakar Kana-Zuru, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kebbi; Alhaji Sani Zauro, shugaban kungiyar dattawan APC na jiha; da Alhaji Faruk Musa-Yaro, Mataimakin Gwamnan Jihar.