A kalla mutane takwas sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon hatsarin mota a Kwana Bakwai dake kan hanyar Minna zuwa Lambatta na jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne a daren jiya juma’a bayan da wata doguwar mota ta yi taho mu gama da wata motar safa ta Sharon Bas dake dauke da mutane goma sha uku wadanda dukkanninsu maza ne.
Kwamandar dake kula da ofishin Hukumar Kiyaye hadura ta kasa FRSC shiyar Lambatta Babatunde Onemola ya ce Musababbin wannan hatsari ya biyo bayan bindiga da tayar mota ce ya yin da kuma aka gaza shawo kan ta.
Jami’an Hukumar waɗanda suka yi uwa da makarbiya wajen ceto wadanda abin ya ritsa da su, sun tabbatar da cewa mutane sha uku ne hatsarin ya ritsa da su.