By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane uku ne suka mutu tare da ceto wasu mutane biyu da ransu a karkashin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Yaba da ke jihar Legas ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa ginin bene mai hawa uku da ake ci gaba da yi ya ruguje inda ya rufta kan wani ginin da ke gefensa a Akanbi Crescent a unguwar Yaba a jihar Legas.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas da wasu masu aikin ceton da suka isa wurin, an ce sun isa wurin ne sa’o’i guda bayan rugujewar domin fara aikin ceto.
Darakta Janar na LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce dukkan gawarwakin da aka gano manyan maza ne, kuma ana ci gaba da kokarin ceton rayuka.
Oke-Osanyintolu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nosa Okunbor, ya fitar mai take, ‘Rahoton Halin da ake ciki kan Rugujewar Gine-gine a Titin Akanbi Kusa da Babban Kofar Unilag’.
Ya bayyana cewa jami’an agajin gaggawar sun kwaso gawarwakin tare da ceto wasu da ke raye sakamakon tura manyan na’urorin hukumar cikin gaggawa.
Sanarwar ta kara da cewa, “An sabunta: An kuma gano wani babba namiji da ya mutu a karkashin baraguzan ginin.
“Jimlar ƙidaya har zuwa karfe 23:00 na safe. An ceto mutane 2 manya maza a raye inda aka samu Matattu 3 manya maza.”
Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto ga sauran wadanda abin ya shafa.