Mutane uku sun rasa rayukansu a wani rikice da ya barke a kauyukan Jahar Neja
A kalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, dayawa kuma sunyi rauni sanadiyyar rikici da ya barke a wasu kauyukan Jahar Neja a Najeriya.
Rikicin ya barke ne tsakanin Mutanen Kauyen Boku da kuma Doko a Karamar Hukumar Lavun dake Jahar Neja.
KARANTA:-A girmama hakkin Nnamdi Kanu, Abaribe
An rusa gidaje da dama a lokacin rikicin, sa’annan mutane sukayi anfani da bindigu da adduna wajan fadan.
Wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya shaidawa Jaridar Thisday “rikicin ya soma ne misalin karfe 5:30 na yammacin yau Laraba, Lokacin da wasu manoma daga Kauyen Doko suna kan hanyar zuwa gona aka ruwaito cewar Mutanen kauyen Boko sun farmake su.”
Dajin hakan su kuma Mutanen kauyen Doko suka bazama don maida martani, in da sanadiyyar hakan mutane uku suku mutu sa’annan mutane da yawa suka samu raunuka.
Wadanda suka raunatan dai an kaisu asibitin dake garin Kutigi wasu kuma asibitin dake Bida.
Kauyukan dai sun shafe shekaru 50 basa ga maciji da juna kan gonaki, wanda tsohuwar Masarautar tayi bakin kokarin wajan sulhunta su amma kawo yanzu basu daina ba.
A halin yanzu dai an umarci kauyukan dazu garzaya zuwa Kotu don yanke hukunci.