By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan lafiya na jihar Ebonyi, Daniel Umezurike, yace ba a tabbatar da mutuwa ko bullar cutar amai da gudawa a al’ummar Ndiegu Amagu dake karamar hukumar Ikwo a jihar ba.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a daren Juma’ar data gabata yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar tantancewa da ya kai Ndiegu Amagu a karamar hukumar Ikwo, inda ake samun rade daradin rahoton bullar cutar.
Yace lokacin da aka fara samun rahoton bullar cutar a farkon watan Nuwamba, jami’an ma’aikatar, da hukumar lafiya ta duniya, da sauran hukumomin da abin ya shafa, sun ziyarci yankin.
“Mun gudanar da gwaje-gwajen bincike cikin sauri kuma duk samfuran da aka gwada sun zama mara kyau sannan kuma mun tura samfuran da aka tattara zuwa dakin gwaje-gwaje a Abuja,” Yace a lokacin da wannan jita-jita ta barke, an tura jami’an da abin ya shafa yankin inda suka yi mu’amala sosai da jama’ar yankin, in ji shi.
Sannan yace, “Mun ziyarci yankin ne da manufar tabbatar da wannan jita-jita, da kula da marasa lafiya a cikinsu, da tattarawa da gwadawa da wayar da kan jama’a kan cutar.
Kwamishinan yace, “An kwantar da sauran mutanen ne a wata cibiyar lafiya dake kusa inda daya daga cikin al’ummar wata mai juna biyu ta nuna alamun cutar, yayin da daya kuma yace ya kwana biyu yana kwance a asibitin.
“Ina ba da tabbacin cewa abokan hulɗar kiwon lafiya da suka dace za su ci gaba da sanya ido kan ci gaba daga yankin da muke shirin ɗaukar duk wani matakin gaggawa.sannan “Ba ma son mutane su firgita ko alakanta mutuwa da da cutar amai da gudawa ko irin wannan cuta, domin a halin yanzu babu ita a jihar Ebonyi.