An tabbatar da mutuwar wani mutum ɗaya a ranar Asabar, a yayinda mutane biyar suka ji raunuka daban-daban, a hatsarin mota a Abuja.
Lamarin ya faru ne kusa da gidan mai na AA Rano, akan hanyar Kubuwa zuwa Abuja da misalin ƙarfe 11 na ranar Juma’a.
Hatsarin ya faru ne da ababen hawa guda 19 da wata babbar mota.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ebonyi: Matasan Suna Zanga Zanga Kan Zargin Kashe Wasu Matasa uku Da Mota Tayi
Haka zalika, majiyar Jaridar Dimokuraɗiyyar tace an ƙone mutane takwas daga cikin ababen hawan, a yayinda guda 11 suka lalace.
Lamarin ya faru ne biyo bayan rasa shawo kan motar da direban tirelar yayi.
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Hanyoyi ta Ƙasa Bisi Kazeem, yace hatsarin ya haɗa da mutane 20 da ababen hawa guda 19.
Yace “mutane 20, da suka haɗa da maza 12, da mata 5, da ƙananan yara guda 3 dasu hatsarin ya rutsa, a yayinda maza uku da mata biyu suka ji raunuka daban-daban.
“Waɗanda suka ji raunukan da wanda ya mutu, an kaisu Asibitin Zankili dake Utako kafin zuwan jami’an Hukumar ya zuwa wurin da lamarin ya faru.