Wata kungiyar ci gaban kasa da kasa ta Sightsavers, ta ce akwai kimanin mutane miliyan 24 da ke fama da rashin hangen abun dake nesa a Najeriya wanda miliyan 1.3 daga cikinsu suka kamu da cutar makanta a shekarar 2020.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar jim kadan bayan da gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirinta na farko na kula da lafiyar ido na kasa domin magance matsalolin da ake samu na makanta da nakasar gani a fadin kasar nan.
Sunday Isiyaku, darektan kungiyar Sightsavers a Najeriya, ya ce manufar za ta taimaka wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiyar ido ga daukacin ‘yan Najeriya tare da rage tasirin zamantakewa da tattalin arziki da nakasar gani ke haifarwa.
Abubuwan da suka sa gaba a cikin sabuwar manufar sun hada da fitar da manufofin zuwa jihohi 36 dake Najeriya, samar da kungiyoyin kula da lafiyar ido na jihohi da za su jagoranci aiwatarwa, horar da kwararrun kiwon lafiyar ido, da tabbatar da samun damar yin aiki mai rahusa ga Yan Nijeriya.
A wani labarin Kuma na daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta karyata labarin da kafafen yada labarai suke yadawa cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma’aurata da yammacin ranar Litinin a Akure, babban birnin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata a Akure.
Kafofin yada labarai sun yi ikirarin cewa an yi garkuwa da ma’auratan kuma aka tsinci gawar mijin a unguwar Odi olowo da ke Akure.
Odunlami, ya bayyana cewa wanda aka kashe din jami’in tsaro ne, wanda direban motar ya kashe shi, inda ya kara da cewa matar marigayin ta kai karar zuwa ga ofishin ‘yan sanda.
“Al’amarin ya faru ne sakamakon hatsarin mota biyo bayan gudun wuce gona da iri kuma mutumin da abin ya faru wani jami’in tsaro ne mai shekaru 60 ko sama da haka.
“Matar wanda abin ya shafa ta bar ofishinmu ba da dadewa ba, don haka babu wani abu da ya faru na sace wasu ma’aurata a ko’ina a Jihar Ondo.
“Labarin wasu ma’aurata da aka yi garkuwa da su a Jihar Ondo da mijin da aka kashe, karya ne. Ina kira ga jama’a da su tabbatar da kowane bayani kafin yada shi,” in ji ta.