By Ishaq Dabai
Wata mata memba a kungiyar agaji ta (YMCN) wanda aka fi sani da Munazzamatul Fityanul Islam ta fadi kasa wanda a sana diyyar faduwar tata ne ya rasa rayuwarta, yayin da wasu 10 suka fadi amma ansami nasarar farfado dasu jiya yayin da kungiyar ta gudanar da jerin gwano don murnar Eid el-Maulud a Abuja.
Dubban Musulmai da suka ƙunshi ɗaliban makarantun Islamiyya, membobin ƙungiyar agaji ta farko da wasu daga sassa daban -daban na babban birnin tarayya Abuja sun yi jerin gwano ta wasu titunan Abuja don zuwa wajen bikin.
A wajen taron, Ministan Abuja, Malam Muhammadu Musa Bello shine wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari.
Da take magana kan lamarin, wata jami’ar ladabtarwa ta kungiyar dake kula da Karamar Hukumar Kuje, Malama Sajida Bala Abdullahi, ta ce marigayiyar mai suna Asma’u yar shekar (20) tazo taron ne daga Kuje.
“Lokacin da na isa wurin da abin ya faru ne na fahimci Asma’u ta fadi a kan hanya kuma an tabbatar da cewa ta mutu.
Shugaban kwamitin shirya taron, Dakta Adamu Muhammadu Inuwa, ya shaida wa manema labarai cewa taron da aka shirya za a kammala da karfe biyu na rana ya kare a baya saboda abubuwan da suka faru.
Malam Muhammad Abani, ma’ajin kungiyar Jama’atu Ahbabul Rasul, reshen Abuja, ya alakanta abubuwan da suka faru da karancin kayan aiki.
Malam Abani yace, “Muzaharar ta fara ne da misalin karfe 7 na safe lokacin da wasu daga cikin mahalarta taron ba suyi karin kumallo ba kuma da yawa daga cikinsu an tsayar dasu a tsaye a cikin rana suna jiran juyawarsu taci gaba zuwa wurin taron.’ ’