Sh
A ranar Alhamis ne, shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya tabbatar da kashe mutum 10 wadanda a cewarsa biyu daga ciki baki ne a rikicin da ya auku a kasar. Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabinsa a gidan Talabijin a birnin Johannesburg.
Shugaban kasar ya ce cikin kwanakin nan kasarsa ta fuskanci rikice-rikice da wadansu bata gari suka afkar, inda suka rika bin baki da ma ‘yan kasa suna afka musu. Ramaphosa ya kara da cewa; mutane sun rasa rayukansu, sannan iyalai da dama sun shiga cikin firgici. Ya ce zuwa yanzu yana mai tabbatar da mutuwar mutum goma ciki kuwa harda baki guda biyu.
Sannan ya ce jami’an ‘yan sandan Afrika ta Kudu, sun kama mutum 80 da mutuwar mutum biyar da ake zargi afkar da wannan rikicin a birnin Johannesburg da babban birnin kasar na Pretoria a ranar Talata. Wanda daga nan rikicin ya sake fadada zuwa wadansu garuruwan.