Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,114 da suka sake kamuwa da korona a ranar Juma’a.
A cewar NCDC, a ranar Laraba kuma an sallami mutum 1,269 daga asibiti bayan sun warke daga cutar sannan annobar ta yi ajalin mutum 27 cikin sa’a 24 da ta gabata.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, Legas ce kan gaba a yawan waɗanda suka kamu da cutar cikin sa’a 24 da ta gabata da mutum 408.
A Kaduna, an samu ƙarin mutum 63 da suka kamu da cutar cikin kwana ɗaya, Oyo kuma an samu mutum 56 sai Borno mai 46.
Imo na da 42, Edo 41, Ogun 37, Rivers 31, Ekiti 25, Yobe 20, Kano 18 da Akwa Ibom 18. Delta da Osun, an samu mutum 15 kowace jiha.
Sauran jihohin sun haɗa da Kwara mutum 11, Bayelsa da Nassarawa dukkansu an samu ƙarin mutum 6 sai Zamfara 4 da kuma Bauchi 1.
Abuja, babban birnin ƙasar na biye da Legas ɗin da mutum 95 sai Plateau mai mutum 90 yayin da a Ondo aka samu mutum 66.
A halin da ake ciki dai jimillar wadanda suka kamu da cutar a ƙasar ya kai 128,674 yayin da kuma aka sallami 102,780, sai kuma mutum 1,577 da suka mutu.