Akalla talakawa da marasa galihu 1,500 ne suka ci gajiyar shirin Tallagin bada magunguna kyauta da rundunar sojojin saman Najeriya ta gudanar a kauyen Lawanti da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe da kewaye.
Rundunar 109 Combat Reconnaissance Group (CRG) dake Gombe ce ta dauki nauyin gudanar da aikin a wani bangare na gudanar da bukukuwan tunawa da cika rundunar sojin sama ta kasa NAF shekaru 58 da kafuwa.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da taron a jiya, Sabon Kwamandan 109 CRG, Air Kwamanda Michael Ekwueme, ya ce a yayin aikin bada magungunan, likitocin sun samu halartar, masu fama da cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, ciwon suga, ulcer, hawan jini, da matsalolin hakori da ido na daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin.
Ya kuma kara da cewa sama da yara 500 ne kuma suka samu sauki daga cututtukan dake damunsu a lokacin gudanar da shirin.
Wanda ya samu wakilcin Laftanar Janar Joseph Udoh, ya ce babban hafsan hafsan sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao ne ya kaddamar da shirin na kula da lafiya domin samar da ayyukan jinya kyauta ga ‘yan uwa marasa galihu da suka karbi bakuncinsu.
A wani labarin Kuma na daban.
Shaye-shayen Muggan Kwayoyi Ne, Ke Rura Kashe-Kashe A Najeriya—– NAPTIP
Darakta, wayar da kan jama’a, na hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), Josiah Emerole, ya ce kashe-kashe domin yin tsafi na, kungiyoyin asiri da tashe-tashen hankula a cikin al’umma ana iya danganta su da shan muggan kwayoyi.
Ya bayyana hakan ne a Abuja Laraba a wani taron bita mai taken ‘Cutar Muggan Kwayoyi, Kisan matsafa da kuma kungiyoyin Asiri a Najeriya’ wanda gidauniyar Katolika Caritas Foundation of Nigeria, African Faith da Justice Network da Dominicans for Justice and Peace suka shirya.
Ya ce taron bitar an yi shi ne da nufin samar da cikakkiyar dabarar da za ta iya magance ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Chigbu Odemulam Chilee, Mataimakin Darakta, Rage Bukatun muggan kwayoyi, wanda ya wakilci Hukumar Yaki da fataucin miyagun Magunguna ta Kasa, ya ce: “Tsarin tarbiyyar yara, al’adu, rashin aikin yi, talauci, damuwa, rashin girman na gaba, takaici da matsi, wasu dalilai ne da ke mutane tunzura mutane shiga cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi.
“A cikin kowane hudu daga cikin masu shan muggan kwayoyi a Najeriya, daya mace ce, kuma daya daga cikin mutane biyar da suka yi amfani da kwayoyi, na fama da matsalar shan muggan kwayoyi. Amfani da miyagun ƙwayoyi ya fi zama ruwan dare tsakanin Matasa masu shekaru 25 zuwa 39.”
Babban jami’in tsare-tsare na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Okechi Robinson, ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi a yanzu ya kai ga daliban sakandire, har ma da daliban firamare da shekarun su ya Kai 10.
Robinson ya ce: “Daya daga cikin hanyoyin magance matsalar ita ce ta yin hukunci mai tsauri kan laifukan miyagun kwayoyi. Mun ga irin wannan yanayin a ƙasashe kamar Singapore, Malaysia da sauran inda hukuncin ya fi tsanani ga laifukan miyagun ƙwayoyi.
“Wannan a fili ya taimaka musu wajen ragewa sosai idan ba a kawar da matsalar muggan kwayoyi ba a wadannan kasashe. Don haka Najeriya na bukatar hukunci mai tsauri don magance laifukan miyagun kwayoyi