Mutane biyu sun kone kurmus a ranar Talata yayin da wasu tankokin mai guda biyu suka fashe sannan suka kama da wuta a jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne a wurin binciken ababen hawa da ke kan hanyar Elele zuwa Owerri a garin Omurelu na karamar hukumar Ikwere ta jihar.
Rahotanni sun nuna cewa, Wutar da ta tashi sakamakon fashewar ta bazu a cikin al’umma, ta lalata gidaje da sauran kadarorin Al’uma
Wasu mazauna unguwar da dama sun samu munanan raunuka sanadiyar lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun farmaki Fadar Masarautar Kagara, da Kasuwa a Jihar Niger
Wani dan asalin yankin Mai suna Innocent Amadi ya ce, lamarin ya faru ne lokacin da wata tankar man fetur ta fadi.
Ya Kara da cewa, tankar mai guda biyu su fadi, inda sukai ta zubar da Mai sannan suka kama da wuta.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Rivers Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce, ba shi da tabbacin adadin yawan wadanda suka mutu.