Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ‘yan kungiyar ta’addancin ta Ansaru a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
Jaridar Daily Trsut ta ruaito a ranar Asabar cewa ‘yan kungiyar suna yin wa’azi ga jama’ar yankin a lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta, inda suka kashe mutanen kauyen biyu.
An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage a gabashin karamar hukumar da nufin fatattakar ‘yan ta’addan.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka mamaye al’ummomin yankin gabashin karamar hukumar, inda suka tsare mutanen kauyen daga hare-haren ‘yan bindiga.
Ishaq Usman Kafai, shugaban kungiyar BEPU na Masarautar Birnin-Gwari, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an dauki tsawon sa’a guda ana arangama tsakanin kungiyoyin biyu.
Ya kara da cewa, ’yan kungiyar ta Ansaru wadanda su ma suna dauke da muggan makamai ne sun yi galaba a kan ‘yan bindigar, wanda hakan ya sanya su (’yan bindiga) suka gudu daga kauyen.
“An samu barna a yayin rikicin – shago, motoci biyu da kuma wani asibiti mai zaman kansa. ‘Yan bindigar ma sun kashe wasu mutanen yankin (ma’aikata) guda biyu yayin da suke tserewa cikin dajin da gudu,” inji shi.
Kafai ya ce asibitin ya kone sakamakon gobarar da ta tashi daga wata mota da ta kone.
Ya ce, ba za a iya tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu a tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan Ansaru ba, amma ya ce mutanen kauyen sun yaba da yadda Mayakan Ansarun suka kare garin daga ‘yan fashi.
Jaridar ta Daiky Trust a ranar Asabar ta kuma kara da cewa daruruwan mazauna garin da suka hada da mata da kananan yara sun tsere daga garin a yayin harin.
Kafai ya ci gaba da cewa, kungiyar ta Ansaru ta ci gaba da wa’azin bayan fafatawar, kuma ta shawarci mutanen kauyen da su samu makamai domin kare kansu daga makiya, tare da yaki da gwamnati domin kafa daular Musulunci.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin gano hakikanin abin da ya faru kafin ya yi tsokaci kan lamarin.