Mutane biyu sun mutu da sanyin safiyar Laraba yayin da wata tankar mai dauke da mai ta fashe a hanyar Legas zuwa Ibadan.
An ruwaito cewa motar da ke dauke da Man (PMS) wacce aka fi sani da fetur ta kama da Wuta ne da misalin karfe 6:05 na safe a gaban kamfanin CDK da ke da nisan kilomita kadan daga mahadar Sagamu a kan babbar hanyar.
Akalla mutane takwas ne da motoci uku hatsarin ya shafa.
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta ranar Laraba.
“Jami’an kashe gobara sun kashe wutar, an karkatar da ababen hawa zuwa sashin Ibadan-Lagos da kuma jami’an FRSC da ke bakin aiki domin kawar da cin koson ababen hawa”.
“An shawarci masu ababen hawa da su yi tuki a hankali, su bi ka’idojin Tuku da kuma ka’idojin hanya” in ji Okpe