Hukumar daƙile cuta masu yaɗuwa ta Tarayyar Afirka CDC ta ce mutum 61,181 suka kamu da cutar korona a ƙasashe 53 na membobin ƙungiyar.
Hakan ya fito ne a bayanan da CDC Afrika ta wallafa a shafinta na Twitter, inda suka kara da cewa; cutar ta kashe mutum 2,234 a ƙasashen Afirka, yayin da kuma mutum 20,932 suka warke daga cikin waɗanda suka kamu da cutar a ƙasashe membobin ƙungiyar Tarayyar Afirka 53.
Cutar ta fi yaɗuwa a Arewacin Afirka, sai kuma yankin yammacin Afirka inda mutum 17,973 suka kamu